Isa ga babban shafi
Wasanni

Messi ya yi ritaya daga buga wa kasarsa kwallo

Gwarzon dan wasan kwallon kafa na Argentina, Lionel Messi ya yi ritaya daga buga wa kasarsa tamaula.

Lokacin da Lionel Messi ya barar da bugun fanareti a wasansu da Chile a gasar Copa America
Lokacin da Lionel Messi ya barar da bugun fanareti a wasansu da Chile a gasar Copa America Adam Hunger-USA TODAY Sports
Talla

Dan wasan ya sanar da haka bayan ya zubar da bugun fanareti a wasan karshe na gasar Copa America da kasar Chile ta doke su .

A cewar dan wasan, ya kawo karshen murza leda a tawagar kasarsa, inda ya ce, ya yi duk abinda da zai iya amma duk da haka ya gaza samun nasara, abinda ya bayyana a matsayin abin bakin ciki a gare shi.

Gabanin bugun fanaretin dai, sai da kasashen biyu suka shafe tsawon mintiuna 120 suna fafatawa ba tare da zura kwallo ba, lamarin da ya sa aka shiga bugun fanaretin, inda Chile ta zura kwallaye 4 yayin da Argentina ta zura kwallaye biyu, kuma a karo na biyu kenan a jere da kasar Chile ke daukan kofin gasar ta Copa America, Inda kuma sau uku kenan da Messi ya yi rashin nasara a wasan karshe na gasar ta Copa America.

Baya ga zinari da ya lashe a wasannin Olympics da aka gudanar a shekara ta 2008 a birnin Beijing, Lionel Messi bai taba lashe wa kasarsa wata muhimmiyar gasa ba.

Ko a shekara ta 2014, sai dai Jamus ta doke Argentina 1-0 a wasan karshe na gasar cin kofin duniya.

A karo na 112 kenan da ya buga wa kasarsa gasar kwallon kafa tun lokacin da ya yi suna a shekara ta 2005.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.