Isa ga babban shafi
Wasanni

Hodgson ya yi murabus daga horar da tawagar Ingila

Mai horar da tawagar kwallon kafa ta Ingila, Roy Hodgson ya yi murabus daga mukaminsa bayan kasar Iceland ta yi waje da su a gasar cin kofin kasashen Turai da ake gudanarwa a Faransa.

Roy Hodgson ya yi murabus ne saboda Iceland ta doke su ci 2-1 a gasar Euro 2016
Roy Hodgson ya yi murabus ne saboda Iceland ta doke su ci 2-1 a gasar Euro 2016 REUTERS/Stefan Wermuth
Talla

A karon farko kenan da Iceland ta halarci wata babbar gasa a tarihita, yayin da ta doke Ingila da ci 2-1 a fafatawar da suka yi jiya a Nice, lamarin da ya bata damar tsallakawa matakin wasan dab da na karshe.

Kasar ta Iceland mai yawan al’umma dubu 330, na a matsayi na 34 a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a duniya amma ta yi abin azo a gani a gasar Euro 2016, domin ma ita ce ta rike Portugal 1-1, lamarin da ya bakanta ran Christiano Ronaldo.

Mr. Hodgson mai shekaru 68 ya ce, lokaci ya yi da ya kamata ya bai wa wani wuri domin ya karbi ragamar horar da tawagar Ingila.

Shekaru hudu kenan da Kocin ke horar da Ingila tun bayan da ya maye gurbin Fabio Capello a shekara ta 2012.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.