Isa ga babban shafi
Wasanni

Italiya ta yi waje da Spain a Euro 2016

Kasar Italiya ta tsallaka matakin wasan dab da na karshe bayan da ta samu nasarar casa abokiyar hamayyarta wato Spain mai rike da kambin gasar ta cin kofin nahiyar Turai.

Italian coach Antonio Conte
Italian coach Antonio Conte Reuters/Alessandro Garofalo
Talla

Kasahen biyu sun tashi wasan na jiya ne 2-0 kuma Giorgio Chiellini da Graziano Pelle ne suka ci wa Italiya kwallayen, lamarin da ya kawo karshen Spain a gasar ta bana.

Wannan nasarar dai na a matsayin ramako kan abinda Spain ta yi wa Italiya a shekara ta 2012, inda ta lallasa ta da ci 4-0 a wasan karshe na wannan gasar ta cin kofin nahiyar Turai.

Mai horar da 'yan wasan Italiya, Antonio Conte ya yi rawa ya rausaya a kusa da filin wasan domin nuna murnarsa da nasarar, yayin da ‘yan wasansa suka yaba masa saboda tsare tsaren da ya basu har suka doke Spain.

Yanzu haka, Italiya za ta kara da Jamus mai rike da kofin duniya a zagayen gaba.
 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.