rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Gasar Cin Kofin Turai Kwallon Kafa Faransa Portugal

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Griezmann ne gwarzon Dan wasa a gasar Euro 2016

media
Antoine Griezmann ne ya fi yawan jefa kwallaye a raga a gasar cin kofin Turai REUTERS/Kai Pfaffenbach Livepic

Dan wasan Atletico Madrid Antoine Griezmann na Faransa ne aka ba kyautar gwarzon dan wasa a gasar cin kofin Turai da aka kammala a jiya inda Portugal ta dauki kofi bayan ta doke Faransa 1 da 0.


Griezmann ne kuma ya karbi takalmin zinari saboda yawan kwallaye 6 da ya jefa a raga a gasar.

Dan wasan dai ya kasance barazana ga duk abokan hammayar da ya hadu da su a gasar.

Sai dai wannan ne karo na biyu cikin wata guda ana doke dan wasan a wasan karshe bayan Real Madrid ta doke Atletico Madrid a wasan karshe da suka fafata a matan Mayu a gasar cin kofin zakarun Turai.

Sannan Griezmann da Dimitri Payet na cikin tawagar ‘yan wasa 11 ta hukumar UEFA hadi da Cristiano Ronaldo da aka fitar cikin makara saboda raunin da ya samu a wasan karshe a jiya Lahadi.

Sau ran ‘yan wasan da suka cika tawagar ta UEFA sun hada da Pepe da Raphael Guerreiro da kuma gwalkifan Portugal. Akwai kuma Gareth Bale da Aaron Ramsy da Joe Allen na Wales.

Sannan akwai Jerome Boateng da Toni Kroos na Jamus.

Rashin nasarar da Faransa ta samu ne dai ya mamaye kanun labaran Jaridun Faransa.

Jaridar Le Parisian ta yi dogon sharhin edita ne akan bakin-cikin da Faransawa suka kwana da shi a jiya.

Sai dai kuma shugaban kasar Francios Hollande ya ce Faransa ce ta yi nasara saboda samun damar kammala gasar ba tare da wata barazanar harin ta’addanci ba.