Isa ga babban shafi
Euro 2016

Portugal ta lashe kofin Turai

‘Yan wasan Portugal sun samu kyakkyawar tarba a Lisbon bayan sun isa gida a yau Litinin, sakamakon nasarar da suka samu na lashe kofin Turai bayan sun doke Faransa ci 1 da 0.

Portugal na bikin lashe kofin Turai
Portugal na bikin lashe kofin Turai REUTERS/Rafael Marchante
Talla

Dubun dubatar mutanen kasar Portugal ne suka mamaye tashar jirgin saman Lisbon domin tarbar ‘Yan wasan da Cristiano Ronaldo ya jagoranta.

Ronaldo da kocin shi Fernando Santos ne suka fara fitowa jirgi dauke da kofin Turai da suka lashe.

Sannan shugaban Portugal ne ya tarbi ‘yan wasan tare da dubban mutanen kasar.

An shafe dare ana biki a Portugal saboda nasarar da kasar ta samu a gasar cin kofin Turai.

Portugal dai ta huce hushin wasan karshe da Girka ta doke kasar a gasar cin kofin Turai da aka gudanar a shekarar 2004.

Dan wasan Atletico Madrid Antoine Griezmann na Faransa ne aka ba kyautar gwarzon dan wasa a gasar da aka kammala a jiya Lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.