rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Olympic Ireland

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An cafke Jami’in wasannin Olympics na Turai

media
Patrick Hickey, babban jami’in kula da wasannin Olympics na kasashen Turai JACK GUEZ / AFP

Yan Sanda a Brazil sun kama wani babban jami’in kula da wasannin Olympics na kasashen Turai Patrick Hickey da laifin sayar da tikitin wasannin ta bayan fage.


Rahotanni sun ce an tsare jami’in domin gudanar da bincike wanda shi ne shugaban kwamitin gasar wasannin Olympics na kasashen Turai kuma shugaban kwamitin kasar Ireland a otel din sa.

‘Yan sandan sun yi wa jami’in ne dirar-mikiya a dakin otel dinsa da birnin Rio.

Kafofin yada labaran Brazil sun ce jami’in mai shekaru 71 ya yi kokarin tserewa amma bai samu sa’a ba.

Ana zargin Jami’in ne da sayar da tikicin ta bayan fage da ya kai kudi dala miliyan uku.
‘Yan sandan Brazil sun kaddamar da bincike bayan sun kwace tikitin shiga kallon wasannin Olympics sama da 1000 musamman a ranar farko ta bude wasannin.

Tikitin da ya kamata a sayar akan dala 1,000 ana sayar da su ne akan dala dubu takwas a bayan fage kuma yawancinsu suna da tambarin Ireland a jikinsu, lamarin da ya sa aka kaddamar da bincike akan shugaban kwamitin wasannin na Olympic reshen Ireland.

An dai samu rarar tikitin shiga kallon wasannin Olympics saboda yadda wasu ‘yan kasar Brazil suka kauraceewa wasannin da kuma ‘yan kasashen waje da suka kaurace saboda barazanar cutar Zika.