Isa ga babban shafi
Turai

Ronaldo ne gwarzon Turai a bana

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo na Portugal shi ne ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Turai a bana bayan ya taimakawa kungiyar shi lashe kofin gasar zakarun Turai da kuma taimakawa Portugal lashe kofin Turai.

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo na Portugal ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Turai a kakar 2015/16
Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo na Portugal ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Turai a kakar 2015/16 REUTERS
Talla

Wannan ne karo na biyu da Ronaldo ke lashe kyautar, bayan ya doke abokin wasan shi ne Gareth Bale na Wales da kuma dan wasan Atletico Madrid Antoine Griezmann.

Ronaldo dai ya jefa kwallaye 9 a gasar Zakarun Turai inda ya yi kafada da Michel Platini.

‘Yar kasar Norway Ada Hegerberg ce ta lashe kyautar a bangaren Mata bayan ta taimakawa Lyon lashe kofin zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.