Isa ga babban shafi
kwallon kafa

An rufe kasuwar ‘Yan wasa a Turai

An rufe kasuwar cinikin ‘yan wasa a Turai, kuma a ranar karshe kungiyoyi sun ci kasuwar kafin wa’adinta ya cika inda aka kashe kudi sama da fam miliyan 155 tsakanin kungiyoyin Premier a ranar karshe.

Chelsea ta sake karbo David Luiz daga PSG
Chelsea ta sake karbo David Luiz daga PSG chelseafc
Talla

A bana kungiyoyin Firimiya sun fi zuba kudi a kasuwar ‘yan wasan fiye da cinikiyar shekarun baya.

Cinikayyar ‘yan wasan da aka yi Ingila a bana ta kai sama da kudi Fam Biliyan 1.17, wanda shi ne adadin kudi mafi girma a tarihi.

Firimiya ta Ingila ce kan kaba wajen kashe kudi a kasuwar ‘yan wasan fiye da sauran Lig na kasashen Spain da Jamus da Italiya da kuma Faransa.

Gasar Seria A ce ta biyu wajen kashe kudi a kasuwar inda kungiyoyin gasar suka kashe yuro miliyan 700.

Chelsea ta sake karbo Luiz

Chelsea ta sake karbo dan wasanta David Luiz wanda ta sayarwa Paris Saint-Germain.

Chelsea ta sake karbo dan wasan ne akan kudi fam miliyan 32, bayan ta sayarwa PSG dan wasan akan kudi fam miliyan 50 a 2014 kudi mafi tsada da aka sayar da wani dan wasan baya a ingila.

Chelsea ta karbo Marcos Alonso a daga Fiorentina akan kudi fam miliyan 23. Sannan Chelsea ta ba Juventus aron dan wasanta Juan Cuadrado na tsawon shekaru uku.

Tottenham ce kuma ta saye Moussa Sissoko na Newcastle akan kudi fam miliyan 30. Tottenham ta doke Everton ne akan dan wasan.

Manchester City kuma ta bude kofa ne ga yan wasanta guda hudu, da ba su cikin lisssafin sabon kocin kungiyar Pep Guardiola.

Seviila ta karbi aron Samir Nasri, yayin da Tuni Joa Hart gwalkifan City ya koma Torino a Italiya.

Leicester City ta sayo Islam Slimani dan wasa mafi tsada da kungiyar ta yo cefane. Liecester ta sayo dan wasan ne daga Sporting Lisbon wanda ya kulla yarjejeniyar shekaru 5.

Mario Balletoli ya koma Nice daga Liverpool.

Kwallaye hudu Ballotelli ya jefa wa Liverpool a raga a haskawa 28, kuma kungiyar ta ba AC Milan aron shi ne a kakar da ta gabata

Arsenal ta ci kasuwar a kurareran lokaci inda ta kashe fam milyan 35 domin sayen dan wasan Jamus Mustafi daga Valencia.

Sannan Arsenal ta ware kudi fam miliyan 17 ta karbo Lucas Perez dan wasan Deportivo La Coruna.

A bana ne dai aka fi kashe kudi a kasuwar ‘Yan wasan a nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.