Isa ga babban shafi
Wasanni

Ifeanyi Ubah ta lashe gasar kalubale ta Najeriya

Kungiyar kwallon kafa ta Ifeanyi Ubah ta lahe gasar cin kofin kalubale ta Najeriya bayan ta samu nasara akan Nasarawa United da ci 5-4 a bugun daga kai sai mai tsaren gida a fafatawar da suka yi a filin wasa na Teslim Balogun da ke jihar Legas a jiya Lahadi.

'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Ifeanyi Ubah da ta lashe gasar cin kofin kalubale ta Najeriya
'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Ifeanyi Ubah da ta lashe gasar cin kofin kalubale ta Najeriya thebreakingtimes.com
Talla

‘Yan wasan dai sun shafe tsawon lokacin da aka kayyade wa wasan ba tare da zura kwallo ko guda ba, abin da ya sa aka kai ga bugun fanariti tsakanin kungiyoyin biyu.

Wasan dai ya samu halartar manyan baki da suka hada da ministan wasannin da matasa na kasar, Solomon Dalung da gwamnan jihar Nasarawa, Umar Tanko Al Al-Makura da wakilan gwamnatin jihar Legas har ma da shugabannin hukumar kwallon kafar kasar karkashin jagorancin Amaju Pnnick.

Yanzu haka dai, Ifeanyi Ubah za ta wakilici Najeriya a gasar cin kiofin kalube ta hukumar kwallon kafar Afrika da za a gudanar a shekara mai zuwa.
 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.