Isa ga babban shafi
Tennis

Murray na iya samun karramawar Sir Andy

Andy Murray na Birtaniya na iya samun mukamin karramawa na Sir Andy daga Sarauniyar Ingila bayan ya doke Novak Djokovic a wasan karshe da suka yi na ATP a filin London O2 Arena a ranar Lahadi.

Andy Murray na Birtaniya
Andy Murray na Birtaniya Reuters/Gonzalo Fuentes
Talla

Wani babban kamfanin caca na Birtaniya William Hill shi ne ya fara shigar da bukatar karrama jarumin na Tennis a jerin sunayen da Sarauniya Elizabeth ta biyu zat a karrama a farkon shekara.

Doke Djokovic dai a gasar London ATP da Paris Masters ya tabbatar da Andy Murray shi zai kasance na daya a duniya a karshen shekarar nan.

Murray ya dade yana fuskantar barazana daga manyan jaruman Tennis na duniya guda uku Novak Djokovic da Roger Federer da Rafael Nadal, yanzu kuma dan wasan na Birtaniya ya nuna kan shi a matsayin jarumin Tennis.

Murray ya lashe Wimbledon da zinari a Olympics a bana.

Yanzu zai shiga sahun jaruman ‘yan wasan Birtaniya irinsu Sir Bradley Wiggins dan tseren keke Sir Alan Suger.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.