rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kwallon Kafa Seria A Premier League League 1 La liga

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransawa sun fi yawa a manyan lig na Turai

media
Paul Pogba na Faransa da ke taka kwallo a Manchester United Reuters / Carl Recine Livepic

Wani sakamakon bincike akan wasanni da aka gudanar ya bayyana cewa Faransawa sun fi yawa da ke taka kwallo a manyan lig na Turai. Yayin da kuma rahoton ya ce ‘yan kasar Brazil ne suka fi yawa a sassan Turai.


Manyan lig na Turai da suka hada da Lig 1 na Faransa da Firimiya na Ingila da Bundesliga na Jamus da Siriya A na Italiya, binciken ya ce Faransa ce ta fi yawan ‘yan wasa da yawansu ya kai 116 inda ta ba Brazil ratar ‘yan wasa biyu.

Argentina ce ta uku da yawan ‘yan wasa 97 a manyan lig na Turai.

Rahoton Binciken da cibiyar nazarin wasanni ta gudanar a Switzerland ya ce kimanin ‘Yan Brazil 469 ne ke taka leda a kasashen Turai 31.

Faransawa ne na biyu da yawan ‘yan wasa 312, sai Spain a matsayi na uku da yawan ‘Yan wasa 201.