Isa ga babban shafi
Brazil

“Kofin Sudamericana na Chapecoense ne”

Kungiyar Atletico Nacional ta Colombia da za ta karbi bakuncin Chapecoense a wasan karshe na lashe wani babban kofin gasar kungiyoyin kudancin Amurka, ta bukaci hukumomin kwallon kafa a yanki su ba kungiyar kofin gasar bayan ta rasa tawagar ‘yan wasanta a hatsarin jirgin sama.

Tawagar Kungiyar Chapecoense ta Brazil da hatsarin jirgin ya kashe a Colombia
Tawagar Kungiyar Chapecoense ta Brazil da hatsarin jirgin ya kashe a Colombia NELSON ALMEIDA / AFP
Talla

‘Yan wasan Kungiyar na kan hanyar lashe wani kofin babbar gasar kwallon kafa da kungiyoyin kasashen kudancin Amurka ke bugawa da ake kira Copa Sudamericana wanda shi ne na biyu bayan Copa Libertadores.

Kungiyar Atletico Nacional ta Colombia ta ce ta saka a tarihinta cewa Chapecoense ce zakarar Copa Sudamericana a 2016.

Kungiyoyin Brazil da dama sun ce za su ba kungiyar Chapecoense aron ‘yan wasa a kakar 2017 domin ci gaba da buga babban lig din kasar

Sannan kungiyoyin sun bukaci a lamunce wa kungiyar ci gaba da buga lig mataki na farko har na tsawon shekaru 3 ba tare da sauka zuwa mataki na biyu ba.

A bana dai Chapecoense tana matsayi na 9 ne a lig din Seria A na Brazil. Kuma kungiyar shigo gasar ne a karon farko a 2014 tun shekarar 1979.

Duniyar kwallon kafa ta shiga jimami a ranar Talata bayan hatsarin jirgin sama da ya fadi dauke da tawagar kungiyar Chapecoense a wani yanki mai tsaunuka kusa da garin Medellin na kasar Colombia.

Mazan jiya da yau Pele na Brazil da Maradona da kuma Lionel Messi da Cristiano Ronaldo ne su suka jagoranci alhinin akan kungiyar Chapecoense Real

Jirgin na kamfanin LAMIA wanda ya fito daga Bolivia ya fadi ne dab da ya sauka a Medillin inda rahotanni suka ce tangardar na’ura ce.

Akwai mutane shida da suka tsira a hatsarin, wadanda ake kula da lafiyarsu a asibiti yayin da 71 suka mutu. Cikin wadanda suka mutu har da ‘yan jaridar wasanni 20.

Murmurewar wadanda suka rayu zai taimaka wajen binciken dalilin faruwar hatsarin.

Wata kafar telebijin ta Bolivia ta nuna hutunan ‘yan wasan a lokacin da suke shirin hawa jirgin.

Rahotanni kuma na cewa jirgin wanda ya fadi shi ne jirgin da ya dauki tawagar Argentina a mako biyu da suka gabata ciki har da Messi a lokacin da suka je buga wasannin shiga gasar cin kofin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.