Isa ga babban shafi
Colombia

Rashin mai ne dalilin hatsarin jirgin da ya kashe ‘Yan wasan Brazil

Hukumomin Colombia sun ce hujjoji na ci gaba tabbatar da cewa mai ne ya kare wa jirgin da ya kashe ‘Yan wasan kungiyar Chapecoense Real ta Brazil a lokacin da jirgin ke kokarin yin saukar gaggawa.

Hatsarin jirgin sama da ya kashe 'Yan wasan kungiyar Chapecoense ta Brazil a Medellin kasar Colombia
Hatsarin jirgin sama da ya kashe 'Yan wasan kungiyar Chapecoense ta Brazil a Medellin kasar Colombia REUTERS
Talla

An samu wani sauti da aka dauka a lokacin da matukin jirgin ke magana da jami’an kula da tashi da saukar jirgin sama na Medellin kafin jirgin ya yi hatsari.

A cikin sautin an ji matukin na fadin cewa mai ya kare inda ya bukaci ya yi saukar gaggawa. Bayan mintina kadan kuma ba a sake jin duriyar matukin ba kan halin da suke ciki.

Wasu rahotanni sun ce jirgin ya kamata ya tsaya ya sha mai a Bagota babban birnin Colombia amma matukin jirgin ne ya ki tsayawa akan tunanin man da ke cikin jirgin zai isa zuwa Medellin.

Jirgin na Kamfanin LAMIA mai lamba 2933 ya yi hatsari ne daren Litinin dauke da tawagar ‘Yan wasan kungiyar Chapecoense Real da ke kan hanyar zuwa buga wata babbar gasar kungiyoyin kasashen kudancin Amurka ta Sudamericana da kungiyar Atletico Nacional ta Colombia a Medellin.

Mutane 71 suka mutu a hatsarin jirgin yayin da 6 suka tsira.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.