Isa ga babban shafi
Wasanni

Jadawalin zagaye na biyu a gasar cin kofin zakaru na UEFA

Hukumar kula da shirya gasar cin Kofin Zakarun Nahiyar Turai UEFA, ta fitar da jadawalin zagayen gasar na biyu inda kungiyoyin kwallon kafa 16 zasu fafata, wanda ta fitar a garin Nyon dake kasar Switzerland.

Talla

Kungiyar da ke rike da kofin gasar Real Madrid zata fafata da Napoli daga kasar Italiya, yayinda Barcelona zata kara da Pari Saint-Germain.

A karo na hudu a jere kungiyar kwallon kafa ta Arsenal zata fafata da Bayern Munich cikin wannan gasa ta cin Kofin Zakarun Nahiyar Turai.

Sauran kungiyoyin da zasu fafata sun hadar da Leicester City-Sevilla, kungiyar Man City da Monaco, Benfica da Borussia Dortmund, FC Porto da kungiyar Juventus, sai kuma kungiyoyin Bayer Leverkusen da Atletico Madrid

Za’a buga zagayen faro na gasar a ranakun 14 da 15, da kuma 21 da 22 ga watan Fabarairu mai zuwa.

Zagaye na biyu na wasannin kuma, za’a buga su ne a ranakun, 7 da 8, sai kuma 14 da 15 ga watan Maris mai zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.