Isa ga babban shafi
Spain

Zidane ya cika shekara guda a Real Madrid

Yau Laraba ne Zinedine Zidane ke cika shekara guda a matsayin mai horar da ‘yan wasan kungiyar Real Madrid ta Spain bayan ya gaji Rafael Benitez da kungiyar ta kora.

Zinedine Zidane kocin Real Madrid
Zinedine Zidane kocin Real Madrid REUTERS/Toru Hanai
Talla

Zidane wanda ya lashe komi a matsayin dan wasa tun daga gasar Zakarun Turai da Kofin duniya da kuma kyautar gwarzon dan wasan duniya ta Balon d’Or, yanzu kuma a matsatin koci a watanni 12 ya lashe kofin zakarun Turai da kofin duniya na kungiyoyin kwallon kafa kada da kuma Super Cup.

Zidane zai yi bikin cika shekara guda ne a wasan da Real Madrid za ta karbi bakuncin Sevilla a gasar Copa del ray da za su fafata a daren yau Laraba.

Zidane zai buga wasan ne a yau kafin ya dawo La liga a 2017 inda ya ke jagorantar teburin gasar kafin karshen 2016 bayan buga wasanni 37 ba tare da samun galabr Real Madrid ba.

Babban kalubalen da dai ke gaban Zidane shi ne kare kofin Zakarun Turai da suka lashe a bara inda babu wata kungiyar da ta kafa wannan tarihin.

sannan wani kalubalen shi ne lashe kofin La liga da Barcelona ta mamaye a ‘yan shekarun nan.

Sai a gobe Alhamis ne Barcelona za ta soma buga wasan farko a 2017 a fafatwwar da za ta yi da Athletic Bilbao a gasar Copa del ray.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.