rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gabon Gasar Cin Kofin Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

El Hadary na ya kafa tarihi a Afcon

media
Essam El Hadary na Masar (Photo : Pierre René-Worms/RFI)

Mai tsaren gidan Masar, Essam El Hadary ya kafa tarihi, in da ya kasance dan wasa mafi yawan shekaru da ya buga gasar cin kofin nahiyar Afrika a tarihi.


El Hadary  ya kafa wannan tarihin ne a fafatawar da kasarsa ta yi da Mali a ranar Talata a gasar cin kofin nahiyar Afrika da ake gudanarwa a Gabon.

El Hadary ya yi wasan ne yana mai shekaru 44 da kwanaki biyu da haihuwa kuma babu wani dan wasa mai wadannan shekarun da ya taba buga gasar a can baya.

Masar da Mali sun yi canjaras a wasan na jiya, in da suka tashi ba kare-bin-damo.