rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gabon Gasar Cin Kofin Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ghana ta doke Uganda a gasar kofin Afrika

media
Dan wasan Ghana André Ayew da ya ci wa kasar kwallo a bugun fanariti a fafatawarsu da Uganda a Gabon Pierre René-Worms / RFI

Kasar Ghana ta doke Uganda da ci daya mai ban haushi a fafatawar da suka yi a jiya a gasar cin kofin Afrika da ake gudanarwa a Gabon.


Andre Ayew ne ya jefa kwallon a bugun daga kai sai mai tsaren gida kafin tafiya hutun rabin lokaci, abin da a yanzu ya bai wa Ghana damar samun maki uku a rukuninsu na D.

Ghana ta samu damar bugun fanariti ne bayan Isaac Isinde na Uganda ya yi wa Gyan Asamoah keta a cikin gidan mai tsaren ragar Uganda.

Yanzu haka Ghana ce ke jan raga a rukunin D sakamakon wannan nasara da ta samu.

Tun bayan fara gasar a ranar Asabar da ta gabata, kasashe uku ne kadai da suka hada da Ghana da Senegal da Jamhuriyar Demokradiyar Congo suka yi nasarar lashe wani wasa.