Isa ga babban shafi
Gabon

An fitar da Gabon a gasar cin kofin Afrika

An fitar da Gabon daga gasar cin kofin Afrika da ta ke karbar bakunci bayan sun tashi wasa babu ci tsakaninta da Kamaru, sakamakon da ya bar Gabon a matsayi na uku a rukuninsu na A da maki 3.

'Yan wasan Gabon a gasar cin kofin Afrika
'Yan wasan Gabon a gasar cin kofin Afrika ©Pierre René-Worms
Talla

Gabon ba ta samu nasara ba a dukkanin wasanninta. Ficewar kasar kuma ana ganin zai ragewa gasar armashi.

Burkina Faso ta doke Guinea Bissau ne ci 2 da 0 a karawar da suka yi a jiya lahadi.

Kamaru da Burkina Faso yanzu suka tsallake zuwa zagayen kwata fainal bayan sun jagoranci rukuninsu da maki 5.

Kamaru da ke saman teburin rukunin za ta hadu ne da Senegal a Franceville a ranar Assabar.

Burkina Faso kuma za ta jita ta ga yadda zata kaya a yau a rukunin B inda Senegal za ta kara Algeria a Franceville, Zimbabwe kuma da Tunisia a Libreville.

Kafin Algeria ta tsallake sai ta samu nasara akan Senegal, tare da fatar Tunisia ba ta ci Zimbabwe ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.