rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Olympic

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hukumar IAAF ta soke damar canjin kasashe ga masu wasannin motsa jiki

media
Shugaban hukumar shirya wasannin motsa jiki ta duniya Sebestian Coe

Hukumar da ke lura da shirya wasannin motsa jiki ta Duniya IAAF, ta soke damar canjin kasashe da ta bawa masu wasannin motsa jiki, umarnin da ya fara aiki nan take.


Shugaban hukumar, Sebastian Coe, ya ce an dauki matakin ne ganin yadda `yan wasannin motsa jiki ke sauya kasashen da su ke son wakilta, a duk lokacin da suka ga dama, musamman daga bangaren `yan nahiyar Afrika, wanda yasa ake wa dokokin hukumar hawan kawara.

A cewar Coe za`a kafa wani kwamiti na musamman da zai yiwa dokokin da suka bawa masu wasannin motsa jiki damar sauya kasashen da zasu wakilta.

Sabanin wasan kwallon kafa , masu wasannin motsa jiki suna da damar sauya kasashen da suke wakilta, ko da kuwa sun riga sun wakilci wata kasar a baya, a matakin wasannin motsa jiki na duniya.