Isa ga babban shafi
Wasanni-Afrika

Nahiyar Afrika ta bukaci gurbin kasashe 10 a gasar cin kofin duniya

Dan takarar neman shugabancin hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika, kuma shugaban hukumar kwallon kafar kasar Madagascar Ahmad Ahmad, ya bukaci FIFA ta bawa nahiyar Africa guraben kasashe 10 daga biyar da zasu rika wakiltarta a gasar cin kofin Duniya.

Dan takarar neman shugabancin hukumar kula da kwallon kafa ta Nahiyar Afrika CAF, Ahmad Ahmad
Dan takarar neman shugabancin hukumar kula da kwallon kafa ta Nahiyar Afrika CAF, Ahmad Ahmad insidethegames.biz
Talla

Kiran dai ya samu goyon bayan daukacin shugabannin hukumomin kwallon kafar nahiyar.

A shekara ta 2026 sabon tsarin fadada yawan kasashen da ke halartar gasar cin kofin duniyar daga 32 zuwa 48 da FIFA ta amince da shi zai fara aiki.

Nahiyar turai dai na neman guraben kasashe 16 daga 13 da zasu rika wakiltarta, yayinda ake sa ran nahiyar Asiya ta samu guraben kasashe 9 daga 4 da take da su a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.