Isa ga babban shafi
Wasanni

Matakin FIFA kan Messi bai kamata ba - Barcelona

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta bayyana rashin jin dadinta kan matakin ladabtarwa da hukumar FIFA ta dauka kan dan wasanta Lionel Messi, inda ta ce hakan rashin adalci ne ga dan wasan.

Lionel Messi yayin fafatwar Argentina da kasar Chile a wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin duniya da za'a yi a kasar Rasha a shekara ta 2018.
Lionel Messi yayin fafatwar Argentina da kasar Chile a wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin duniya da za'a yi a kasar Rasha a shekara ta 2018. REUTERS/Marcos Brindicci
Talla

FIFA ta haramtawa Messi bugawa kasarsa wasanni 4 a jere ne sakamakon samunsa da ta yi, da laifin furta kalaman cin zarafi ga mataimakin alkalin wasa yayin fafatawarsu da kasar Chile a ranar Alhamis, wanda kuma suka yi nasarar da 1-0.

Ko da yake Messi zai cigaba da bugawa Barcelona wasanni, kungiyar ta ce abin mamaki ne a ce FIFA ta dauki matakin mai tsauri kan Messi, dan wasan da ta bayyana a matsayin abin koyi ga saura a ciki da kuma wajen filin wasa.

Zuwa yanzu Argentina ta koma matsayi na biyar daga na hudu a rukunin kasashen kudancin Amurka da ke neman cancantar zuwa gasar cin kofin duniya a Rasha, yayinda kuma ta ke bukatar kasancewa daga cikin kasashe hudu na farko.

Wasanni hudu ya ragewa Argentina a sharer fagen neman cancantar, yayinda Messi ba zai bugawa kasar tasa wasanni 3 ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.