rfi

Saurare
  • Rayuwa - A karance
  • Karshe log
  • RFI Duniya

Wasanni Ingila Gasar Zakarun Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Arsenal zata iya halartar gasar zakarun turai - Wenger

media
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger. Reuters / Dylan Martinez

Mai horar da kungiyar Arsenal, Arsene Wenger ya ce, yana da kwarin gwiwa kan cewa kungiyar taasa zata kammala wasaninta na gasar Premier a matakin kungiyoyi hudu na farko.


Ko da yake Wenger, ya amince akwai aiki babba a gaban ‘yan wasansa kafin cimma wannan buri, kasancewar akwai tazarar maki 7 tsakaninsu da kungiyar Manchester City da ke a matsayi na 4 a gasar Ingilar, yayinda Arsenal din ke a matsayi na 6.

To sai dai a cewar Kocin, cimma wannan buri ba sabon abu bane a wajenshi kasancewar ya saba kai kungiyar wannan mataki a tsawon shekaru 20 da ya shafe yana horar da ita.

Yanzu dai lokaci ne kawai zai fayyace ko wannan buri na kocin Arsenal zai cika ko kuma akasin haka.