rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

RFI League 1 Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yan wasan Afrika 13 na takarar lashe Kyautar Marc-Vivien Foé ta RFI

media
Marc-Vivien Foe fitaccen tsohon dan wasan Kamaru ne

An fitar da sunayen yan wasan Afrika 13 da ke taka kwallo a gasar Lig 1 ta Faransa inda cikinsu daya zai lashe kyautar Marc-Vivien Foé a bana wacce RFI da France 24 ke bayarwa duk shekara.


A ranar 15 ga watan Mayun 2017 za a bayar da kyautar a hadin guiwa tsakanin kafar radiyon RFI da kuma kafar telebijin ta France 24.

RFI da France 24 sun fara bayar da kyautar ne a 2009, kuma Marouane Chamakh na Morocco ne ya fara lashe kyautar.

Vincent Enyeama na Najeriya ya taba lashe kyautar a 2014.

A bara Sofiane Boufal na Morocco ne ya lashe kyautar, kuma a bana akwai Dan wasan Nice Younes Belhanda na Morocco cikin yan wasan Afrika 13 da ke takarar lashe kyautar.

Akwai kuma Yan kasar Ivory Coast guda uku da yan kasar Senegal biyu cikin zaratan yan wasan na Afrika 13 da ke taka kwallo a Lig 1.

Yan wasan 13 dai sun fito ne daga kungiyoyin Lig 1 guda 9 kuma yan kasashen Afrika 9 da za a zabi gwarzo daga cikinsu.

Ga jerin yan wasan 13.

• Serge AURIER (Côte d’Ivoire/Paris Saint-Germain)
• Younès BELHANDA (Maroc/OGC Nice)
• Ryad BOUDEBOUZ (Algérie/ Montpellier HSC)
• Famara DIEDHIOU (Sénégal/SCO Angers)
• Karl TOKO EKAMBI (Cameroun/SCO Angers)
• François KAMANO (Guinée/Girondins de Bordeaux)
• Benjamin MOUKANDJO (Cameroun/FC Lorient)
• Steve MOUNIÉ (Bénin/Montpellier HSC)
• Cheikh NDOYE (Sénégal/SCO Angers)
• Jean Michaël SERI (Côte d’Ivoire/OGC Nice)
• Giovanni SIO (Côté d’Ivoire/Stade rennais)
• Julio TAVARES (Cap-Vert/Dijon FCO)
• Steeve YAGO (Burkina Faso/Toulouse FC)