Isa ga babban shafi
Wasanni

Jamus ta tsare wanda ake zargi da kai wa Dortmund hari

Bayan harin da aka kai wa motar da ke dauke da tawagar kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund, yanzu haka mahukuntan Jamus na tsare da wani da suke zargin yana da hannu da harin da aka kai jiya a lokacin da kungiyar ke shirin karawa da Monaco a gasar cin kofin zakarun Turai.

Jamus ta tsaurara matakan tsaro bayan hari a kan ayarin tawagar kungiyar Borussia Dortmund
Jamus ta tsaurara matakan tsaro bayan hari a kan ayarin tawagar kungiyar Borussia Dortmund Reuters / Carl Recine Livepic
Talla

Akwai wasika da ‘yan sandan Jamus suka samu a inda aka kai wa motar tawagar kungiyar Borussia Dortmund hari, kuma masu bincike sun ce wasikar na kunshe da daukar alhakin abun da ya faru.

Sai dai babu cikakken bayani game da wasikar, koda yake kafofin yada labaran Jamus sun danganta wasikar da harin da IS ta dauki alhaki na Berlin da aka kai kasuwar kirsimeti a watan Disemba inda mutane 12 suka mutu.

Yanzu haka dai ana tsare da mutun guda da ake bincikensa a kan alakarsa da fashewar abubuwa guda uku a jiya, yayin da ake binciken ko harin nada alaka da na ta’addanci.

'Yan sanda kuma na farautar wani mutum guda. Kuma jami'an tsaron sun ce an yi kokarin kai wa tawagar Borussia Dortmund hari ne.

Akwai dan wasan kungiyar guda Marc Bartra dan Spain da ya samu rauni da wani dan sanda bayan fashewar abubuwan da ake tunanin bom ne, da ya fashe a lokacin da ‘yan wasan suka kama hanyar zuwa filin wasansu domin fafatawa da Monaco a gasar cin kofin zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.