rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Ingila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dole mu jinjinawa Sanchez - Wenger

media
Alexis Sanchez yayin murnar zura kwallon a ragar kungiyar Manchester City a filin wasa na Wembley. Reuters / Carl Recine

Mai horar da kungiyar Arsenal Arsene Wenger, ya jinjinawa dan wasansa Alexis Sanchez, bisa bajintar da yayi na sharara kwallon da ta basu damar fidda kungiyar Manchester City daga gasar cin kofin FA na Ingila.


Sanchez ya samu nasarar ce yayinda aka shiga mintunan karin lokaci, yayin karawar da suka yi da City a wasan kusa dana karshe na gasar cin kofin FA, a ranar Lahadin da ta gabata.

Karo na 20 kenan Arsene Wenger na samun nasarar jagorantar Arsenal zuwa wasan karshe na gasar cin kofin FA.

Yayinda yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP Wenger ya ce yana fatan Sanchez ya sake rattaba hannu kan yarjejeniyar cigaba da zama a Arsenal.