rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Ingila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Chelsea ta cigaba da jan ragamar gasar Premier

media
'Yan wasan kungiyar Chelsea yayin murnar samun nasarar zura kwallo ta 3 da suka yi a ragar Southampton. Reuters / John Sibley

Kungiyar Chelsea ta cigaba da dafe matsayinta na farko a taburin gasar Premier ta kasar Ingila, bayan samun nasarar maida tazarar maki 7 da ke tsakaninta da mai biye da ita kungiyar Tottenham.


A wasan da ta fafata tsakaninta da kungiyar Southampton bayan da ta karbi bakuncinta a filin wasa Stamford Bridge a jiya, Chelsea ta lallasa Southampton da kwallaye 4 da 2.

Kafin wasan dai tazarar da Chelsea ta baiwa kungiyar Tottenham da ke biye da ita a matsayi na biyu a teburin gasar Premier ta ragu daga maki 7 zuwa 4, sakamakon rashin nasarar da ta yi a hannun Manchester United da kwallaye 2-0.

Wasannin da za’a buga yau a gasar Premier sun kunshi wanda za’a fafata tsakanin Arsenal da Leicester City, Middlesbrough da Sunderland sai kuma kungiyar Crystal Palace da Tottenham.