Isa ga babban shafi
Boxing

Joshua da Klitschko za su dambace a Wembley

Hankalin duniya zai koma Wembley a Ingila a gobe Asabar inda za dambace tsakanin dan damben Birtaniya Anthony Joshua da kuma fitaccen dan damben duniya na Ukraine kasar Wladimir Klitschko.

Anthony Joshua na Birtaniya da Wladimir Klitschko na Ukraine kafin su dambace a Wembley
Anthony Joshua na Birtaniya da Wladimir Klitschko na Ukraine kafin su dambace a Wembley REUTERS
Talla

Damben dai na lashe damarar gasar damben duniya ne ta IBF da Joshua ke fatar kare kambunsa bayan ya lashe WBA.

Ana dai dangaganta damben a matsayin mafi girma da za a gudanar a Birtaniya tsakanin ‘yan damben biyu na duniya da za a gudanar a filin Wembley mai daukar ‘yan kallo sama da dubu 90.

'Yan damben biyu za su kwashi kudi sama da fam miliyan 10 a damben.

Masu sharhi dai na ganin Joshua matashi dan shekaru 27 dan asalin Najeriya na iya doke Klitschko mai shekaru 41 da ya shafe watanni 17 ba ya dambe.

Klitschko na son farfado da martabarsa tun bayan kashin da ya sha a hannun Tyson Fury na birtaniya a 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.