Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Arsenal ta doke Manchester United

Arsenal ta doke Manchester United ci 2-0 a emirate a fafatawar da suka yi gasar premier ta Ingila. Karon farko ke nan da Arsene Wenger ya doke Mourinho a gasar bayan wasanni 13 suna haduwa da juna.

Granit Xhaka da Danny Welbeck ne suka ci wa Arsenal kwallayenta biyu a ragar Manchester United
Granit Xhaka da Danny Welbeck ne suka ci wa Arsenal kwallayenta biyu a ragar Manchester United REUTERS
Talla

Wenger da Mourinho sun dade suna gaba da juna, tun lokacin da Mourinho na Chelsea.

Bayan kammala wasan a jiya, Mourinho ya ce karon farko ke nan da ya fice Emirate ana murna a Arsenal, ba kamar yadda suka saba kuka ba, idan ya shigo Emirate.

Yanzu Arsenal da ke matsayi na 6 a tebur ta datse yawan makin da ke tsakaninta da United da ke matsayi na biyar zuwa maki biyu.

Maki hudu ne kuma ya raba Arsenal da Manchester City da ke matsayi na hudu.

Yakin shiga gasar zakarun Turai ne dai yanzu ake yi tsakanin City da United da Arsenal.

Amma Arsenal nada kwanten wasanni guda biyu.

Mourinho ya ce fatan shi na zuwa gasar zakarun Turai ta hanyar lig ya kawo karshe bayan ya yi barin maki uku a gidan Arsenal.

Manchester na iya samun wuri a gasar zakarun Turai idan har ta lashe kofin Europa.

A ranar litinin ne Chelsea zata buga wasanta da Middleborough, kuma idan Chelsea ta samu nasara zai kasance maki uku ya rage ta lashe kofin Premier na bana.

A ranar Juma’a Tottenham ta sha kashi a hannun West Ham ci 1-0.

Chelsea na iya bikin lashe kofin a cikin makon nan Idan ta samu nasara a gidan Middlesbrough a yau da kuma West Brom a ranar Juma’a.

Zai kasance kofin Antonio Conte na farko a kakarsa ta farko a Stamford Bridge.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.