rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Ingila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

“Ko yanzu kasuwa ta watse dan koli yaci riba” - Mourinho

media
Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho Reuters/Darren Staples

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho, ya ce ko da kungiyarsa bata yi nasara ba, a wasan da zata yi da kungiyar Ajax; wasan karshe da zasu fafata na gasar Europa, kwalliya ta biya musu kudin sabulu a kakar wasa ta bana.


Idan har Mourinho mai shekaru 54, ya samu nasarar lashe gasar Europa, zai zama mai horarwa na farko a tarhin United da ya samu irin wannan nasarar a kakar wasan farko da ya fara aiki.

A watan Fabarairu mai zuwa United zata barje gumi da Ajax a wasan da duk wanda yayi nasarar zai samu halartar gasar cin kofin zakarun kungiyoyin kwallon kafa na nahiyar turai.

A kakar wasan Premier na bana Mourinho ya samu nasarar buga wasanni 25 a jere ba tare da an samu nasarar kan United ba, kafin Arsenal ta kawo karshen hakan, bayan samun nasara kansu da ta yi a 2-0 a ranar Lahadin da ta gabata.