rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Premier League Ingila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kokarin Neman Na 4 A Ingila Ya Kara Zafafa

media
'Yan wasan kungiyar City a lokacin karawarta da United REUTERS

Kungiyoyin kwallon kafa a Ingila na ci gaba da fafutukar ganin sun kare a matakin da bai gaza na 4 ba domin samun damar shiga gasar cin kofin kungiyoyin zakarun nahiyar Turai a kaka mai zuwa.


Gurbi 2 ne ya rage biyo bayan nasarar lashe gasar da Chelsea ta yi, inda kuma Tottenham ta samu adadin makin da ya tabbatar ma ta da gurbin shiga gasar. Yanzu dai Manchester City, Liverpool, Arsenal, da kuma Manchester United ke neman karewa a mataki na 4.

Saura wasanni biyu suka rage a gasar bayan buga wasanni 36 da akayi, Manchester City na mataki na 3 a teburin Premier da maki 72, Liverpool ta hudu da maki 70, Arsenal ta biyar da maki 69 sai kuma Manchester United ta shida ta maki 65 duk da yake ta nada kwanten wasa daya.

Chelsea ta lashe gasar ta Premier a wannan shekara bayan samun nasara akan Westbrom da ci daya da nema a ranar Juma’a da ta gabata.