Isa ga babban shafi
Wasanni-Spain

Real Madrid Zata Sabinta Kwantiragin Zidane

Real Madrid na shirin karawa kocinta Zinedine Zidane wa’adin ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekara ta 2020. Sakamakon irin nasarorin da kungiyar ke samu tun lokacin da ya karbi jagorancinta a watan Janairun shekara da ta gabata.

Mai horar da Real Madrid Zinadine Zidane tare da Cristiano Ronaldo da kuma Sergio Ramos
Mai horar da Real Madrid Zinadine Zidane tare da Cristiano Ronaldo da kuma Sergio Ramos
Talla

A cikin wannan lokaci dai, Zidane ya samu nasarar lashe kofin kungiyoyin zakarun Turai, sannan a wannan kakar kwallo ta bana, kungiyar ta Real Madrid ta kai matakin wasan karshen gasar inda ta ke jiran wasan karshe da Juventus ta Italiya, ga kuma yunkurin lashe gasar La liga da kungiyar ke kokarin yi, ganin cewa kungiyar na neman maki 7 a cikin wasanni 3 da suka rage domin lashe gasar da ta da kwashe shekaru 5 bata samu ba.

Duk da wannan karamci da kungiyar ke son yiwa Zidane, kocin ya bulla yana cewa ‘samun nasarori sune kadai zasu tabbatar maka da aikin ka a Real Madrid’.

Idan kungiyar ta yi nasarar lashe kofin gasar kungiyoyin zakarun Turai da kuma gasar La liga zai kasan ce karon farko tun bayan shekaru 59 da kungiyar ta lashe kofunan guda 2 a lokaci daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.