rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Ingila Gasar Zakarun Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kada ku kwance min zani a kasuwa - Wenger

media
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger. Reuters/Stefan Wermuth

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger, ya roki magoya bayan kungiyar, da su yi fitar dango zuwa filin wasan da kungiyar zata fafata da kungiyar Sunderland a gobe Talata.


Kiran na Wenger na zuwa ne bayanda ta bayyana wasu daga cikin magoya bayan kungiyar ta Arsenal suna kokarin jan ra’ayin mafi rinjayen magoya bayan, su kauracewa uwa kallon wasan na ranar Talata, domin tilastawa hukumar gudanarwar kungiyar ta Arsenal sallamar Wenger daga mukaminsa na mai horar da kungiyar.

Wasanni uku suka ragewa Arsenal a kakar wasa ta bana, wasannin sun kunshi wanda zasu fafata da Sunderland a ranar Talata, sai kuma tsakaninsu da Everton duka a wasannin Premier.

Sai kuma wasa na uku tsakaninsu da kungiyar Chelsea da ta lashe kofin gasar Premier ta Ingila, a wasan karshe na gasar cin kofin FA.

A tsawon shekaru 21 da suka gabata karkashin jagorancin Wenger, Arsenal ta saba kammala gasar Premier a cikin kungiyoyi hudu na farko, wanda hakan ke bata damar samun halartar.

Sai dai nasarar da kungiyar Liverpool ta samu kan West Ham da kwallaye 4-0 a ranar lahadin da ta gabata, ya sanya dole Arsenal ta jira rashin nasarar, Manchester City ko kuma Liverpool din kafin samun damar halartar gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar turai.