Isa ga babban shafi
Wasanni-Jamus

Jamus: Babu hannun kungiyar IS a harin da aka kai wa Dortmund

Tawagar jami’an tsaron da ke bincikar harin da aka kai wa motar ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund da ke Jamus, da wasu abubuwa masu fashewa a ranar 11 ga watan Afrilu daya gabata, ta ce babu wata alama da ke nuna cewa ‘yan ta’adda ne suka kai harin kamar yadda ake zargi a baya.

Motar 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund da aka kai wa hari a abubuwan fashewa a kasar Jamus.
Motar 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund da aka kai wa hari a abubuwan fashewa a kasar Jamus. Reuters
Talla

Tun a lokacin da aka kai harin ne dai, jami’an ‘yan sandan Jamus suka sanar da gano wata wasika da aka yasar a dai dai wurin da harin ya auku.

To sai da a lokacin jami’an sun ki bayyana abinda wasikar ta kunsa, kasancewar sun ce sai sun tantance gaskiyar lamari.

Daga bisani ne dai jami’an suka ce wasikar na dauke da sakon cewa mayakan ISIS ne suka kai harin, to amma bayan kammala bincike sun ce babu gaskiya cikin abinda wasikar ke dauke da shi, barazana ce kawai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.