rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Chelsea ta lashe gasar Frimiya da maki 93

media
Chelsea ta yi bikin daga kofin Frimiyar Action Images via Reuters/John Sibley Livepic

Chelsea ce ta samu nasarar lashe gasar Frimiyar Ingila da maki 93 kamar yadda Real Madrid ta samu nasara kuma wannan ne karon farko tun 1979 da wata kungiya ta samu nasara a gasar da wasanni 30 ko fiye da haka.


Tottenham ta biyu da maki 86 Sai Manchester city ta Uku da maki 78.

Liverpool ta hudu da maki 76, sai Arsenal ta biyar da maki 75, Manchester Utd kuma ta shida da maki 69.

Wannan ne dai karon farko tun 1979 da Manchester United da kuma Arsenal suka kasa karewa a matakin na daya zuwa na hudu.

Matsalolin Arsenal sun kara ta'azara a fili bayan da kungiyar ta kasa samun gurbi a gasar cin kofin kungiyoyin zakarun Turai a karon farko a cikin kusan shekaru 20.

Kungiyar ta Arsenal za ta yi asarar Dala miliyan 50 na kudin shiga sakamakon rashin samun mataki na hudu a lig din.

Magoya bayan kungiyar na neman canjin Arsene Wenger domin ciyar da kungiyar gaba, dama kwantiragin Wenger zata kare a wannan shekara kuma ba za a san makomar sa ba, har sai bayan wasan karshe na cin kofin kalubale FA da kungiyar zata kara da Chelsea a ranar Asabar.