rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni La liga Premier League

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Akwai yiwuwar na koma Manchester Unite-Griezmann

media
Antoine Griezmann REUTERS/Christian Hartmann Livepic

Dan wasan gaba na Faransa da ke taka leda a Atletico Madrid Antoine Griezmann ya tabbatar da yiwuwar komawarsa Manchester United don ci gaba da murza tamaula.


A wata hira da ya yi kafar talabijin ta TMC, Griezmann mai shekaru 26 ya ce, akwai yiwuwar ya koma buga gasar Premier ta Ingila daga La Liga ta Spain.

A lokacin da dan jaridar ya bukaci Griezmann da ya bada makin da bai wuce 10 ba game da yiwuwar komarsa Manchester United, sai dan wasan ya zabi 6 bisa 10.

Sannan kuma ya ce, nan da makwanni biyu zai yanke shawara game da makomarsa.

Griezmann dai shi ne  ya yi na uku wajen lashe kyautar gwarzon dan wasa a bana bayan Christiano Ronaldo da kuma Lionel Messi.

Sannan ya buga wa Faransa wasanni 41 tun daga shekarar 2014, yayin da ya ci wa kungiyarsa ta Atletico Madrid kwallaye 26 a cikin wannan kakar duk da cewa ta kare a matsayi na uku a La Liga.