rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Brazil

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kame tsohon shugaban kungiyar Barcelona

media
Sandro Rosell tsohon shugaban hukumar gudanarwar kungiyar FC Barcelona. REUTERS/Albert Gea/File Photo

Jami’an tsaro sun kame sohon shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Sandro Rosell, bisa zarginsa da hannu wajen sace wasu kudade da ya kamata yi shiga lalitar tawagar kwallon kafa ta kasar Brazil.


A Talatar nan ce, jami’an tsaron suka kai samame gidan Rosell da ke kudancin yankin Catalonia a kasar Spain, inda aka kame wasu mutane 3 baya ga shi kansa, Rosell da matarsa da jami’an sukai awon gaba da su.

Na dai zargin Rosell mai shekaru 53 da yin sama da fadi, da wasu makudan kudade, a lokacin da ya jagoranci bada kwangilar samar da kayayyakin wasa ga tawagar kwallon kafar Brazil, da kamfanin Nike ya samar a waccan lokaci.

Bayan kammala aikinsa ne a shekara ta 2010 ya zama shugaban hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona a kasar Spain.