rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kwallon Kafa Premier League

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Conte na son Wenger ya ci gaba da horar da Arsenal

media
Kocin Chelsea Antonio Conte da na Arsenal Arsene Wenger squawka.com

Kocin Chelsea Antonio Conte ya ce Arsene Wenger ya cancanci ci gaba da aikin horar da Arsenal saboda nasarorin da ya samu a shekaru 20 da ya shafe yana horar da kungiyar.


Tsokacin kocin na Chelsea na zuwa ne kafin haduwarsu da Wenger a gobe a wasan karshe na lashe kofin FA.

A karon farko cikin shekaru 20, Wenger ya kasa tsallakar da Arsenal zuwa gasar zakarun Turai.

Wenger dai na harin lashe wa Arsenal kofin FA na 7, akan haka Conte ke ganin ba adalci ba ne Arsenal ta raba gari da kocinta.

Wasu na ganin wasan karshe da Arsenal za ta buga da Chelsea a gasar FA ne wasan Wenger na karshe a matsayin kocin Arsenal.

Conte ya ce Wenger ya nuna shi kwararren manaja ne a shekaru 20 da ya kwashe yana aikin horar da kungiyar Arsenal.