rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ghana za ta fafata da Mali a wasan 'yan kasa da shekaru 17

media
Tambarin hukumar kwallon kafar Afirka CAF

An fitar da kungiyar kwallon kafa ta kasar Nijar wato Mena daga gasar neman kofin Afirka ta matasa ‘yan kasa da shekaru 17, sakamakon kashin da ta sha a hannun ‘yan wasan Ghana a bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan zagayen kusa da na karshe.


An dai tashi wasan ne Ghana na da ci 6 yayin da Nijar ta zura kwallaye 5 a filin wasa na Port Gentil da ke kasar Gabon.

A yanzu dai za a yi karawar karshe ne tsakanin Ghana da Mali a ranar lahadi mai zuwa, inda Nijar za ta kara da Guinee Conakry domin neman matsayi na uku a wannan gasa. Ghana dai ta taba daukar wannan kofi har sau biyu.