rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Saudiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dan Wasan Kwallon Kafa na Man. United Paul Pogba na Umra a Saudiyya

media
Dan wasan Manchester United Paul Pogba Reuters / Andrew Couldridge

Dan Wasan kwallon kafa da yafi kowane dan kwallon kafa tsada a duniya Paul Pogba na kasar Saudiya yanzu haka yana aikin Umra.

 


Paul Pogba ya isa kasar Saudiya tun jiya Asabar, kuma ya tafi birnin Makka inda kafofin yada labarai na Saudiya suka nuna shi yana ayyukan ibada.

Kwanaki uku ke nan Paul Pogba ya daukaka Clob din nasa Manchester United a wasan da suka buga da AFC Ajax a Stockholm.