rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Premier League

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Huddersfiled ta shiga gasar Premier ta Ingila

media
'Yan wasan Huddersfield Town tare da kocinsu David Wagner REUTERS

Kungiyar kwallon kafa ta Huddersfield ta samu nasarar shiga babbar gasar Premier ta Ingila bayan ta doke Reading da ci 4-3 a karamar gasar Lig ta kasar.


Huddersfiled ta casa Reading ne a bugun daga kai sai mai tsaren gida a fafatawar da suka yi a ranar Litinin a Wembley, in da suka fara shafe tsawon mintina 120 ba tare da jefa kwallo ko guda ba, abin da ya sa aka kai ga bugun Fanariti.

Tun dai shekarar 1972, raban da Huddersfield ta shiga gasar Premier ta Ingila, sai a wannan karon.