rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Premier League Gasar Zakarun Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wenger na dakon makomarsa a Arsenal

media
Kocin Arsenal Arsène Wenger REUTERS/Rebecca Naden

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger ya gana da mai kungiyar Stan Kroenke, a yayin da ake dakon sanin makomarsa ta ci gaba da horar da kungiyar ko kuma raba gari da ita.


Babu dai cikakken bayani dangane da sakamakon ganawar tasu, amma ana saran sanar da matakin da za a dauka kan Wenger a taron Darektocin kungiyar a wannan Talata.

A wannan kakar ne kwantiragin Asrene Wenger zai kare bayan ya jagoranci kungiyar na tsawon shekaru 21.

Rahotanni sun ce, Kocin na son ci gaba da zama a kungiyar, amma yana fuskantar matsi da caccaka saboda halin da Arsenal ta tsinci kanta a ciki, musamman na rashin samun gurbi a gasar zakarun Turai a kaka mai zuwa, bayan ta kammala gasar Premier ta Ingila a mataki na biyar.