rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Premier League Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wenger zai ci gaba da horar da Arsenal

media
Kocin Arsenal Arsene Wenger REUTERS

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya sanya hannu kan sabuwar kwangilar shekaru buya inda zai ci gaba da aikinsa na horar da ‘yan wasan kungiyar. Wannan dai shi ya kawo karshen cece-kucen da aka dade ana yi kan makomar Wenger a Arsenal.


Wasu magoya bayan Arsenal ba su ji dadi ba musamman wadanda ke ganin sallamar Arsene Wenger shi ne kawai zai kawo sauyi a kungiyar.

A bana Arsenal ta sha kashi ci 10-2 a gida da waje a wasanta da Bayern Munich a gasar zakarun Turai

A karon farko cikin shekaru 20 Arsene Wenger ya kasa tsallakar da Arsenal zuwa gasar cin kofin zakatun Turai.

Amma a bana Wenger ya lashe kofin FA bayan doke Chelsea a wasan karshe.

Bukatar Arsenal dai ita ce lashe kofin Premier da kofin zakarun Turai, kuma shugabannin kungiyar sun ce sun yi imanin Wenger na iya cim ma burin kungiyar.

An dai shafe shekaru 13 Arsenal ba ta lashe kofin Premier ba a karkashin jagorancin Wenger ba.