rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Chelsea ta samu Fan milyan 150 a karshen gasar Firimiya

media
'Yan wasan Chelsea Action Images via Reuters/John Sibley Livepic

Kungiyar Chelsea wadda ta lashe kofin Firimiya a bana, ta samu kudaden da yawansu ya kai Fan milyan 150, kimanin dalar Amurka milyan 190 a matsayin tukuici, karin fiye da kashi hamsin cikin dari na abin da aka bai wa Leicester lokacin da dauki wannan kofi a gasar firamiya ta bara.


An dai samu wadannan kudade ne sakamakon kulla yarjeniyoyi da kamfanoni da kuma gidajen talabijin don yin tallace-tallace da kuma sauran kyaututuka da ake samu lokacin gudanar da gasar.

A jimilce dai an samu kudaden da yawansu ya kai fan bilyan 2 da milyan 400 a bana, wadanda aka raba wa kulob 20 da suka shigar gasar ta Firimiya.

Tottehham, wadda ta zo ta biyu a bana, ta samu fan milyan 145, to sai dai abin ta sama bai kai wanda aka bai wa Manchester City da kuma Liverpool ba, sakamakon kyaututuka masu nasaba da yin amfani da filayen wasanninsu da kuma yawan lokutan da suka bayyana a gidajen talabijin da dai sauransu.