rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni UEFA

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Real Madrid ta kafa tarihin lashe kofin gasar UEFA a jere

media
Tawagar 'yan wasan kungiyar Real Madrid bayanda suka lashe kofin gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar turai. Reuters / Carl Recine Livepic

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe kofin gasar zakarun kungiyoyin nahiyar turai, bayan da ta samu nasarar kan takwararta ta Juventus da kwallaye 4 – 1, a fafatawar da suka yi jiya a filin wasa da ke birnin Cardiff na Wales.


Wannan nasara da Madrid ta samu, yasa ta samu kafa tarihin zama kungiya ta farko, da ta lashe kofin sau biyu a jere, a gasar ta UEFA, zalika ta cigaba da rike kambunta na zama kungiyar da ta fi lashe kofunan gasar ta zakarun kungiyoyin nahiyar turai, bayan da ta lashe kofi na 12 a jiya.

Dan wasa Critiano Ronaldo ne ya samu nasarar jefa kwallaye biyu, yayinda Casemiro ya jefa guda a ragar Juventus.

Karo na biyar kenan, kungiyar Juventus na samun nasarar zuwa wasan karshe a gasar ta cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar turai, amma bata samun nasarar lashe kofin.