rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tiote na Ivory Coast ya rasu yana atisaye

media
Cheick Ismael Tiote na Ivory Coast REUTERS

Tsohon dan wasan Newcastle United Cheick Tiote ya rasu yana da shekaru 30 da haihuwa bayan ya yanke jiki ya fadi a yayin atisaye a China kamar yadda mai magana da yawunsa ya sanar a wannan Litinin.


Marigayin kuma dan asalin Ivory Coast ya shafe tsawon shekaru bakwai yana buga wa Newcastle tamaula, in da ya buga ma ta wasannin league-league 138.

A cikin watan Fabairu ne ya koma kungiyar Beijing Enterprises ta China akan kudin da ba a bayyana adadinsa ba.

Sannan ya na cikin tawagar Ivory Coast da ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afrika a shekarar 2015.