rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hazard na Chelsea na jinyar watanni uku

media
Dan wasan Chelsea Eden Hazard na jinyar watanni uku Reuters/Toby Melville

Dan wasan gaba na Chelsea Eden Hazard zai yi jinyar watanni uku sakamakon tiyatar da aka yi ma sa a kafarsa ta dama saboda raunin da ya yi.


Dan wasan mai shekaru 26 ya samu raunin ne a yayin atisaye da tawagar kasarsa ta Belgium gabanin fafatawar da ta yi da Jamhuriyar Czech a wasan sada zumnuta.

Wannan dai na nufin cewa, za a fara gasar Premier ta Ingila a kaka mai zuwa ba tare da dan wasan ba.

A rabar 12 ga watan Agusta mai zuwa ne ake saran shiga sabuwar kakar Premier a Ingila.

Eden Hazard ya taimaka wa Chelsea wajen lashe kofin Premier a bana, in da ya ci ma ta kwallaye 16 a cikin wasanni 36.