rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni La liga Spain

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Pepe ya yi sallama da kungiyar Real Madrid

media
Messi rike da kwallo a kafar shi Pepe na Madrid na biye da shi. REUTERS/Susana Vera

Dan wasa mai tsaron baya na kungiyar Real Madrid Pepe, ya sanar da kawo karshen zamansa a kungiyar cikin wata zantawa da yayi da manema labarai a Spain.


Matakin na Pepe, ya kawo karshen shekaru 10 da ya shafe yana bugawa kungiyar Real Madrid wasa.

Kungiyoyin Paris St-Germain da AC Milan sun dauki lokaci suna zawarcin dan wasan da haifaffen kasar Brazil ne amma yake bugawa Portugal wasa.

Zalika wata majiyar ta ce akwai wasu daga cikin kungiyoyin da ke fafata gasar Premier League ta kasar Ingila ma na zawarcin Pepe.

Pepe ya bugawa Real Madrid wasanni 334, tare da shi kuma kungiyar ta lashe kofunan gasar Laliga ta Spain 3 da kuma na gasar zakarun kungiyoyin nahiyar turai 3.