Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Manchester United ta fi Real Madrid kudi

Manchester United ta sha gaban Real Madrid a matsayin kungiyar da ta fi kudi a duniya a cewar Mujallar Forbes. United ta karbe matsayin ne a karon farko cikin shekaru biyar.

Tsadadden dan wasa a duniya Paul Pogba na wasan Manchester United
Tsadadden dan wasa a duniya Paul Pogba na wasan Manchester United REUTERS
Talla

Forbes ta ce darajar kudin Manchester ta kai dala biliyan 3.69.

Kungiyar Barcelona ce ta biyu da darajar kudi dala biliyan 3.64.

Daga matsayi na daya Real Madrid ta koma matsayi na uku da darajar kudi dala biliyan 3.58

Bayern Munich ce ta 4, amma kungiyoyin ingila 5 na cikin jerin manyan kungiyoyi 10 masu kudi da suka hada da Manchester City da Arsenal da Chelsea da Liverpool da kuma Tottenham.

Juventus ta Italiya ce a matsayi na 9 amma PSG ta Faransa na matsayi na 11.

Ronaldo ya fi karbar kudi a duniya

Mujallar Forbes ta ce Cristiano Ronaldo ne dan wasan da aka fi bayan kudi a duniya.
Shekara ta biyu ke nan a jere dan wasan na Real Madrid ke jagorantar teburin ‘yan wasan masu kudi a duniya.

Ronaldo na karbar kudi dala miliyan 93 na albashi da sauran kudaden lada. Kuma kudaden da ya ke karba sun karu da sama da dala miliyan 5 a shekara.

Abokiyan hammarysa na Barcelona Lionel Messi ne na uku a jerin attajiran yan wasan na duniya.

LeBron James dan wasan kwallon Kwando ne na biyu da ke karbar kudi sama da dala miliyan 83.

Messi na karbar kudi dala miliyan 80 a shekarar da ta gabata.

Akwai yiyuwar Messi ya kere Ronaldo a badi idan ya sanya hannu kan sabuwar kwantaragi da Barcelona.

Binciken na Forbes ya shafi kudaden da ‘yan wasa ke samu a wasanni 11.
Kuma ‘yan wasan kwallon Kwando ne a sahun gaba cikin jerin yan wasa 100 da suka fi samun kudi.

Roger Federer, dan wasan kwallon Tennis ne na hudu a duniya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.