rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tennis Roland Garros

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Nadal ya lashe Roland Garros karo na 10

media
Rafael Nadal ya lashe kofi na 10 a Roland Garros RFI/Pierre René-Worms

Rafael Nadal ya kafa tarihi a gasar Roland Garros da ake gudanarwa a Faransa inda ya lashe kofin gasar karo na 10 bayan ya doke Stan Wawrinka a wasan karshe da suka gabata a jiya Lahadi.


Nadal ya doke Wawinka ne ci 6-2, 6-3, 6-1 inda ya kasance mutun na farko da ya lashe kofin babbar gasar Gram slam sau 10.

Nadal ya ce yana cike da farinciki domin lashe kofi karo na 10 wani abu muhimmi ne a rayuwarsa.

Kofunan manyan kgasannin tennis 15 Nadal ya lashe, inda ya ke bi ma Roger Federer da ke da yawan kofunan 18.

A bangaren mata, ‘yar kasar Latvia Jelena Ostapenko ce ta lashe kofin gasar bayan ta doke Simona Halep ta Romania ci 4-6, 6-4, 6-3 a wasan karshe da suka fafata a ranar Asabar.