rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Nijar Cote d'Ivoire Najeriya ‘Yan gudun Hijira

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan gudun hijira sun bunkasa Nassara Agadez

media
'Yan wasan Nassara Agadez na Nijar na atisaye tare da 'yan gudun hijira gettyimages.com/Issouf Sanogo

Wata karamar kungiyar kwallon kafa a Nijar mai suna Nassara Agadez ta bunkasa sakamakon wasu ‘yan gudun hijira da suka zama sabbin ‘yan wasanta.


‘Yan gudun hijirar da akasarinsu suka fito daga Najeriya da Cote d’Ivoire sun isa Agadez ne da zimmar neman hanyar ratsawa zuwa nahiyar Turai amma hakarsu ba ta cimma ruwa, lamarin da ya sa suka yanke shawarar taka leda a wannan kungiya da ke buga karamar gasar League a Nijar.

Daya daga cikin sabbin ‘yan wasan da ya fito daga Cote d’Ivoire Mohammed Diaby ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa, shugaban kungiyar, Bachir Ama ya yi ma sa alkawarin tafiya da shi Turai muddin ya buga wa kungiyar kwallo a tsawon kaka guda.

Diaby, kwararren dan wasa da ya samu horo a wata babbar makarantar kwallon kafa a Abidjan ya ce, burinsa shi ne zuwa nahiyar Turai don ci gaba da murza tamaula.

A halin yanzu dai, kungiyar ta Nassara Agadez na biyan ‘yan gudun hijirar albashin CFA dubu 100 kwatankwacin Dala 170, sannan kuma ta dauki nauyin makwancinsu.

Sabbin ‘yan wasan sun hada da ‘yan Najeriya hudu da ‘yan Cote d’Ivoire hudu.